A yayin wani bikin da aka gudanar a a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja wanda aka ke kira International Conference Centre a ranar Laraba, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.
Abubakar ne dan takarar babbar jam'yyar adawa ta PDP a zaben 2019 inda ya kara da shugaba Muhammadu Buhari na APC.
A cikin jawabin sa a yayi taron, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattijai da na matasa.
Ya kuma yi alkawarin mayar da hankali kan ɓangarori biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da jihohin kasar gaba da kara musu ikon gudanarwa."
Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta gaza, yana mai cewa akwai bukatar 'yan Najeriya su ba shi hadin kai don a ceto kasar daga rugujewa, zargin da gwamnatin Buhari ta sha musantawa.
Abubakar mai shekaru 75, ya yi rikon mukamin mataimakin shugaban kasa Olusegun Obasanjo har tsawon wa'adi biyu.
Abubakar yana neman ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai kammala wa’adinsa na biyu kuma na karshe a watan Mayun 2023.
Ana shirin gudanar da zaben shugaban kasa ne a ranar 25 ga watan Fabrairu.