ABUJA, NIGERIA - Hakanan jam’iyyar ta kafa kwamitin mutum 37 da zai tsara raba mukamai a tsakanin shiyyoyin siyasa, duk da wasu manyan ‘yan jam’iyyar na son a bar takarar a bude.
PDP dai ta sanya Naira miliyan 40 a matsayin kudin fom din takarar shugaban kasa miliyan 21 ga takarar gwamna, miliyan 3.5 takarar sanata, miliyan 2.5 ga ‘yan majalisar wakilai, inda gaba daya mukaman a ka rage kashi 50% ga matasa daga shekara ta 25-30.
Duk da haka shugaban nakasassu na jam’iyyar Akilu Abdullahi Jugnu ya ce kudin sun wuce kimar da masu karamin karfi da nagarta za su iya biya.
Alhaji Abubakar Jibrin da ke jagorantar tawagar ‘yan kasuwa daga arewa maso gabas, ya ce sun dau matakin sayawa Atiku fom din ne don karfafa ma sa guiwar sake gwada takarar kamar yanda ya yi a 2019.
Dan kwamitin amintattu na PDP Sanata Abdul Ningi ya yi tsayin daka cewa har a wannan karo, arewa ce za ta tsaida dan takarar shugaban kasa don haka ne mafi zama adalci.
Gaba daya hukumar zabe za ta karbi sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyu zuwa 3 ga watan yuni sannan in Allah ya kai mu 25 ga Febrerun badi a gudanar da zaben.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya: