Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan siyasar a jihar Kano suka bijirewa umarnin rundunar ‘yan sandan jihar, lamarin da ya haifar da arangama tsakanin magoya bayan su.
Mataimakin sufeton ‘yan sandan mai kula da shiyya ta daya dake Kano AIG Bello Sani Dalijan ya fadawa manema labarai jim kadan bayan ganawa da jami’an rundunar a shalkwatar su dake Bompai cewa, lallai ne su kiyaye mutuncin aikin su da na rundunar, kamar yadda babban sufeton na ‘yan sanda ya bada umarni.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan ta Kano ta haramtawa Jam’iyyun APC da PDP da kuma NNPP gudanar da tarukan a lokaci guda wato ranar Alhamis din nan, saboda kaucewa tarzoma.
To amma duk da haka, an samu karanbatta tsakanin magoya bayan APC da na NNPP, inda rahotanni suka ce mutane da dama sun jikkata kuma mazauna birnin Kano da kewaye sun kasance cikin zullumi.
Hon. Ibrahim Zakari Sarina, Sakataren reshen jihar Kano na Jam’iyyar APC ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya kira su taro kuma bayan rashin jituwa da juna ya sanar dasu cewa, ya soke dukkanin tarukan guda uku domin zaman lafiya.
Sai dai Farfesa Rufa’I Ahmad Alkali dake zama shugaban NNPP na kasa ya ce dama ce ga sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya je gida domin yin gangami a matsayin sa na dan takarar shugaban kasa, kuma abin da suka tsara kenan tsawon lokaci, amma jin zai zo ne wasu Jam’iyyu suka bijiro da nasu taron da gangan domin kawo masa cikas.
Koda yake wadanda aka raunata na ci gaba da karbar magani a asibitoci, bangarorin biyu dai na ci gaba da nuna yatsa ga juna. Hakan ta sanya zauren hadin kan Malaman Kano fitar da sanarwar jan hankali ga mazauna jihar ta bakin sakataren Zauren Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, game da muhimmancin gudanar da zabe cikin lumana. Zauren ya kuma yi kira ga al’umar Kano su fita su kada kuri’a ga mutanen da suke so bisa yanayi na kiyaye doka da oda.
Al’umar gari dai na gudanar da harkokin su cikin yanayi na taka-tsantsan, yayin da sa’o’I kalilan suka rage a tafi rumfunan zabe domin kada kuri’a ga sabon shugaban Najeriya da ‘yan majalisar dokokin kasar.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5