An kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a yawancin mazabun da ke birnin tarayya Abuja da kewaye da ma wasu sassan kasar, baya ga wurare kalilan da aka samu matsaloli da suka sa akan dole aka dage zaben zuwa Lahadi, kamar yadda aka yi a wasu mazabu hudu a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.
A wasu wuraren an fara zaben a makare sakamakon rashin isowar jami’an aikin zabe da kuma kayan aiki da wuri.
A wata mazaba a jihar Nasarawa, rahotanni sun bayyana cewa har zuwa karfe uku na yamma jami’an aikin zabe basu isa wurin ba. Hakazalika a unguwar Lube da ke Abuja, bayan rashin zuwan kayan aiki da wuri an kuma fuskanci tangardar na’ura, lamarin da ya sa komai ya tsaya har sai da aka kai dare ana aikin zaben.
Wani mazaunin unguwar Lube da ya kada kuri’arsa, ya shaida wa babbar Editar Sashen Hausa na Muryar Amurka Grace Alheri Abdu cewa, sai wajen karfe 10 na dare ya samu damar kada kuri’a duk da cewa ya isa rumfar zabe wajen karfe 7 na safe.
A wasu yankunan kasar, ciki har da birnin Tarayya Abuja, an tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin da ake gudanar da zaben, amma duk da haka jama’a basu fasa kada kuri’arsu ba, lamarin da ya sa wasu ke gani zaben bana zai zo da canji.
Ya zuwa yanzu dai ba za a yi hanzarin cewa ga wanda ke kan gaba ba a zaben, ko da yake kafafen sada zumunta na bayyana sakamakon wasu mazabu da hukumar INEC ba ta kai ga tantancewa ba tukun. Sai dai wani batu da yake tabbas shi ne, duk mazabar da ta kammala kidayar kuri’u ta san wanda ya lashe zaben mazabar.
Wannan zaben dai ya na daya daga cikin zabukan da aka yi cikin lumana a Najeriya duk da cewa an fuskanci tashe-tashen hankula a wasu wuraren, amma ba kamar zaben baya ba.
Saurari hirar da Ibrahim Garba ya yi da Grace Alheri Abdu:
Your browser doesn’t support HTML5