Shugaban ya yi imanin cewa wadanda suka yi wannan aika-aika, a Awkunanaw, dake karamar hukumar Enugu ta Kudu a Jihar Enugu, ba su mutunta rai da mutuncin dan Adam, don haka dole ne za su fusknacin fushin Allah kuma zai hukunta su.
Shugaban kasar ya tabbatar da kudurinsa na ganin an gudanar da zaben da babu tashin hankali.
Ya tunatar da duk ‘yan siyasa cewa zabin masu kada kuri’a ne ke da muhimmanci, don haka duk ‘yan Najeriya da suka cancanta su jajirce wajen gudanar da ‘yancinsu na ‘yan kasa ba tare da jin tsoron wani ba.
Shugaban ya umurci hukumomin tsaro da su bi diddigin wadanda suka aikata wannan danyen aiki, duk da cewa ya jajantawa iyalan wanda aka kashe, da kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da kuma jam’iyyar Labour Party.
Shugaba Buhari ya yi addu’a Allah ya jikan wanda ya rasu.
Tuni dai hukumar INEC ta dakatar da zaben dan takarar sanata na jam’iyyar Labour a mazabar Enugu ta Gabas.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja, babban birnin tarayya.
A cewarsa, zaben da aka shirya yi na gundumar a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023, an dage shi zuwa ranar 11 ga Maris, 2023.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja, babban birnin tarayya.
A cewarsa, zaben da aka shirya yi na gundummar a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023, an daga shi zuwa ranar 11 ga Maris, 2023.