Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Zaben Shugaban Kasa A Wasu Mazabun Jihar Bayelsa Zuwa Lahadi


Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Hukuma zaben Najeriya ta INEC ta ce an dage gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya na ranar Assabar zuwa Lahadi a wasu mazabun jihar Bayelsa.

Yayin da yanzu haka aka soma kidaya kuri'un zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a mafi akasarin rumfunan zabe a fadin Najeriya, an jinkirta gudanar da zaben a wasu mazabun jihar Bayelsa har zuwa ranar Lahadi.

Hakan ko ya biyo ne bayan hatsaniya da ta barke a yayin soma gudanar da zabe a mazabu 4 da suka kumshi rumfuna zabe 141 a Yenagua babban birnin jihar, lamarin da ya sa tilas aka jingine kada kuri'a.

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai a babbar cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja da yammacin ranar Assabar, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ya zuwa lokacin, jami'an tsaro sun sami shawo kan rikicin.

To sai dai kuma ya ce a yayin da ake shirin ci gaba da soma zaben, jami'an zabe wadanda akasarinsu 'yan hidimar kasa ne na NYSC, sun bayyana fargabar ci gaba da aikin a cikin yanayin.

Wasu a layin kada kuri’a
Wasu a layin kada kuri’a

Yakubu ya ce wannan ne ya sa aka jingine aikin a yau Assabar, tare da zimmar bai wa jami'an tsaro damar tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, tare kuma da tsara sake gudanar zaben a rumfunan da lamarin ya shafa a gobe Lahadi.

Ko baya ga jihar Bayelsa, Farfesa Yakubu ya ce an sami rahotannin hatsaniya a wasu rumfunan zabe a jihohin Delta, Abia da Imo da ke kudu maso gabashin Najeriyar.

A jihar Kebbi ma an sami ta da rikici a wasu mazabu na Birnin Kebbi da Argungu, yayin da kuma wani rikicin ya barke a wasu mazabu na karamar hukumar mulki ta Safana a jihar Katsina, wanda yayi sanadiyyar rasa wasu na'urorin tantance masu kada kuri'a na hukumar wato BVAS.

Sai dai hatsaniyar a wadannan wuraren ba ta kai ga dakatar da zaben ba.

Haka ma hukumar ta rasa wasu na'urorin na BVAS a jihohin Delta da Anambra.

To amma shugaban hukumar ta INEC ya ce tuni da jami'an tsaro suka sami nasarar kwatowa tare da dawo da na'urorin.

Masu kada kuri’a
Masu kada kuri’a

A jihar Edo kuma an dage zaben 'yan majalisar tarayya zuwa mako 2 na tafe, wato ranar zaben gwamnoni ke nan, sakamakon kuskuren da aka samu wajen buga takardun jefa kuri'a.

Shugaban INEC ya ce akwai wani dan takara da aka lura sunan sa ya bayyana a takardar rubuta sakamakon zabe, amma kuma hoton jam'iyyarsa bai fito ba a takardun kada kuri'a.

Farfesa Yakubu ya ce hukumar ta INEC ta tattauna da dukkan shugabannin hukumomin tsaron kasa, inda ta bayyana musu matukar bukatar kara tamke damarar tabbatar da tsaro, musamman a yayin da aka tunkari matakin tattara sakamkon zabe.

Ana sa ran za'a soma aikin tattara sakamakon zaben daga jihohi a daren yau Assabar ko da sanyin safiyar gobe Lahadi

XS
SM
MD
LG