ZABEN 2015: Sarkin Musulmi Ya Yabawa Shugaban Kasa Akan Zabe

Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III

A wata fira da wani gidan talibijan Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya yabawa shugaban kasa da cika alkawarin da ya sha yi masu dangane da zabe

Sarkin Muslmi Muhammad Sa'ad Abubakar III yace hakika Shugaba Goodluck Jonathan ya tsayarda gemu ga maganarsa inda ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe wanda zai tabbatar da zaman lumana a Najeriya tare da kokarin kaucewa zubda jini.

Sarki Sa'ad yace wannan abun da shugaban kasa ya yi babban karamci ne hakan ya nuna domin irin abun da ya sha fada a tarukansu dashi. Yace ya tuna a haduwarsu ta karshe shugaban ya jaddada tabbatar da matsayinsa kuma gashi a yanzu ya bayyana a fili ta hanyar rungumar kaddara tare da mika al'amari da nasara ga wanda ya lashe zaben, wato Janar Buhari.

Sultan yaci gaba da cewa yana ganin wannan babban daratsi ne ga shugabanni da kowa ma. Akan irin tasirin da matsayin shugaba Jonathan zai haifar Mai Martaba yace yana ganin duniya zata fahimci cewa yanzu fa Najeriya ta taka turbar iya dimokradiya kuma akwai bukatar a kara ginata. Yace irin halin da shugaban kasa ya nuna alama ce ta cigaban dimokradiya a kasar. Yace ya yi amannar Najeriya zata anfana da hakan.

Dangane da zaben Mai Martaba Sa'ad Abubakar III yace hakika an gudanar da zaben cikin lumana a yawancin kasar. Ya kara da cewa ya ga jami'an tsaro da na zabe suna nuna halin dattaku. Ya yiwa Ubangiji godiya domin zaben shi ne mafi sahihanci da aka taba gudanarwa a kasar. Wannan ne karo na farko tun lokacin da aka kafa dimokradiya a kasar shugaba mai ci zai rungumi kadara har ma ya taya wanda ya kayar dashi murna. Lamarin ka iya ba shugaban mai barin gado farin jini ciki da wajen Najeriya.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Sarkin Musulmi Ya Yabawa Shugaban Kasa Akan Zabe - 2' 17"