Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga ‘yan najeriya da su gudanar da zabe na gari yayin da kasar ke tunkara manyan zabuka a wannan asabar mai zuwa.
Mr. Obama ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su kaucewa rikici irin wanda ya gurbata zabukan da kasar ta yi a baya.
A wani faifan bidiyo da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, Mr Obama y ace zabe na gari na daga cikin matakan da za su iya kawo karshen kungiyar Boko Haram, wanda hakan zai baiwa ‘yan gudun hijra komawa muhallansu.
“Ina kira ga dukkanin shugabannin da ‘yan takara su gayawa magoya bayansu cewa tashin hankali bashi da hurumi a tsarin dimokradiya, kuma su tabbatar da cewa ba za su saka kansu akan wani abu da ya shafi rikici kafin zabe da lokaci zabe da bayan zabe.”
Ya kuma kara kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama su hada kai su yi biris da masu kiran a ta da hankali.
“Idan aka yi zabe lami lafiya, hurumin kowa da kowa ne ya ga cewa an zauna lafiya koda wanene ya ci zaben.” In ji Obama.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi takarar sake neman shugabancin kasar ne da Janar Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
A zaben shekarar 2011, rikici ya barki a wasu sassan kasar bayan da aka yi zargin cewa an yi magudin zabe yayin da ‘yan takarar biyu suka nemi shugabancin kasar.