Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: PDP Ta Samu Goyon Bayan Wasu Jam'iyyu a Adamawa


Malam Nuhu Ribadu dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkshin PDP
Malam Nuhu Ribadu dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkshin PDP

Duk lokacin zabe 'yan siyasa kan fitar da sabbin dabaru domin samun nasara kamar abun da ya faru a jihar Adamawa.

Makon da ya gabata wasu 'yan takaran gwamna a jihar Adamawa na jam'iyyun APGA da COWA da NCP da kuma MPP suka fito suka ce sun janyewa dan jam'iyyu PDM Dr. Ahmed Modibo.

Saidai tun kafin a je koina sai kuma 'yan jam'iyyun suka sake bulla a gidan jam'iyyar PDP inda suka fito suna marawa dan takarar jam'iyyar Nuhu Ribadu baya. Alhaji Abdunasir Umar Haman dan takarar gwamnan na jam'iyyar MPP ya bayyana dalilansu na goyon bayan Nuhu Ribadu.

Haman yace su a jam'iyyun hudu sun zauna sun yi nazari tare da hangen nesa sun gane cewa babu wanda zai iya yin tafiyar da suke so a yi sai Nuhu Ribadu. Yace can baya sun yi kuskure kuma suna neman gafara daga mutanen Adamawa.

Rebaran Ibrahim Dauda Iro mataimakin dan takarar gwamna na jam'iyyar COWA yace su basu san Nuhu Ribadu ba. Basu da wata alaka dashi. Amma sun kirashi sun gaya masa cewa auren farko da suka yi kuskure ne. Sun warware wancan auren yanzu sun dawo wurin Nuhu Ribadu.

'Yan bangaren Ribadu suna cike da murna domin sabon kamu da suka yi. Alhaji Saidu Halilu sakataren kemfen din Nuhu Ribadu yace jam'iyyun sun duba wanda zai kawowa jihar nasara sun gane saidai Nuhu Ribadu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

ZABEN2015: PDP Ta Samu Goyon Bayan Wasu Jam'iyyu a Adamawa - 3'28"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG