Bayan da rahotanni suka fara bayyana alamar Janar Muhammad Buhari na kan hanyarsa ta lashe zaben ne matasa suka fara yin murna.
Janar Buhari ya lashe zaben da aka yi a ranakun Asabar da Lahadin da suka shude.
Matasan da aka zanta dasu sun yi matukar farin ciki suna yiwa sabon shugaban fatan alheri domin ya samu nasara da jin dadin mulkinsa. Sun hada da yiwa Allah godiya wanda ya baiwa Janar Buhari nasara. Sun yi fatan sabon shugaban zai cika adalci.
Dattawa ma ba'a barsu a baya ba wajen nuna gamsuwa da sakamakon zaben wanda ya tabbatar da nasara ga Janar Muhammad Buhari. Sun ce sun dade suna rokon Allah Ya nuna masu irin wannan ranar. Yau sai gashi Allah ya tabbatar.
Dr Saidu Ahmed Dukawa wani masanin kimiyar siyasa na jami'ar Bayero Kano a tsokacin da ya yi kan zaben yace zaben ya nuna dimokradiyar Najeriya ta daga zuwa wani mataki na gaba. Daya daga cikin matsalolin dimokradiya shi ne a ce gwamnati mai ci ta ki yadda ta fadi zabe. To amma sai gashi shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zaben ya kuma nuna murna. Abu na biye dashi shi ne talakawan Najeriya sun samu nasara domin sun dade suna neman canji. Jajircewar da suka yi ya nuna sabon shugaban zai samu goyon bayan talakawan kasar.
Ga raohoton Ibrahim Mahmud Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5