Duk da ikirarin wasu kafofin labaru wakilin APC a zauren bada sakamakon zaben a Abuja Dr.Hakeem Baba Ahmed yace sun zura ido tukun.
Dr Hakeem yace suna jiran sauran sakamako. Wuraren da suka ji kamar an samu miskila basu ga sakamakonsu ba tukunna. Yace baya son yace abu yayi daidai ko bai yi daidai ba ko kuma ya zargi kowa yanzu.
Dangane da ko suna kan gaba Dr Hakeem yace sun fi so su ga an fito da sakamakon gaba daya na duk jihohi 36 da Abuja. Yace inda suka ga akwai gyara suna nan suna rubutawa. Akan shirye-shirye da ka'idodi an gaya masu kuma sun fahimcesu.Yace suna nan suna binsu da fatan Allah ya sa a gama lafiya.
Akan lashe zabe Dr Hakeem yace da yaddar Ubangiji sun riga sun lashe ko. Allah yasa a yi masu adalci -inji Dr Hakeem, a baiwa mutane abun da suka zaba. Mutane sun nuna suna neman canji. Yace Allah ya baiwa hukumar zabe karfin zuciya tayi gaskiya, tayi adalci.
A wani abu tamkar mayarda martani PDP tace bata damu da yadda APC tayi gagarumin nasara a raewa maso yamma ba. APC ta samu kuri'u kusan miliyan biyu a Kano inda PDP ta tashi da dubu dari biyu da 'yan kai kacal. Oliseh Metuh kakakin PDP yace sun san zasu lashe zaben domin hukumar zabe bata sanarda kasar yankunan da shugaba Jonathan ke da rinjaye ba.
Wani abun mamaki shi ne yadda PDP ta lashe jihar Nasarawa wadada gwamnanta dan jam'iyyar APC ne. To amma sakataren SDP Sadiq Abubakar ya kalubali yawan kuri'un da aka soke. Yace an soke kuri'u dubu saba'in da tara. Kamata yayi a je a sake zabe a wuraren da aka soke masu kuri'u.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5