Babban jami’in fadin sakamakon zaben Shugaban Kasa a Jihar Oyo, Furfesa Ayo Salami na Jami’ar Ile-Ife y ace mutane miliyan biyu da dubu dari uku da arba’in da hudu da dari hudu da arba’in da takwas ne su ka yi rajista a jihar sanna aka tantance miliyan daya da dubu saba’in da uku da dari takwas da arba’in da tara. Furfesa Salami ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari (murabus) shi ne kan gaba da kuri’u dubu dari biyar da ashirin da takwas da dari shida da ashirin, a yayin da kuma jam’iyyar PDP ta su Shugaba Goodliuck Jonathan ta zo ta biyu da kuri’u dubu dari uku da uku da dari uku da saba’in da shida.
Don haka babban jami’in bayyana sakamakon zaben na jihar Oyo Furfesa Salami y ace a matsayinsa na babban jami’in bayyana sakamakon zaben ya na mai rattaba hannu kan wannan sakamakon zaben, kamar yadda wakilan jam’iyyu su ma su ka sa hannu a kai.
Wakilinmu na jihar Oyo Hassan Ummaru Tambuwal ya ruwaito wakilin jam’iyyar APC Mr. Iyola Oladokun na cewa tun ranar Asabar su ke wajen su na zuba ido tare da karbar sakamakon zaben . Shi kuwa waklin jam’iyyar PDP wadda ta sha kasa y ace shi dai an bashi sakamakon zabe amma ba ya da ta cewa.
Bugu da kari, jam’iyyar APC ce ta lashe dukkannin kujerun Majalisar Dattawa uku da kuma na wakilai 12 daga cikin 14, hatta guda biyun da su ka rage, jam’iyyar Labor party ce ta ci.