Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Gwamna Babangida Aliyu Na Jihar Naija Ya Fadi Zaben Sanata


Muazu Babangida Aliyu.
Muazu Babangida Aliyu.

A cigaba da rikitowa da manyan 'yan siyasa ke yi a wannan zabe na Najariya, Shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya Mu'azu Babangida Aliyu ya fadi zaben sanata.

Yayin da hukumar zabe ke cigaba da tattara sakamakon zaben Shugaban kasa a jihar Naija, Gwamnan jihar kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muazu Babangida Aliyu ya sha kasa a takarar kujerar Sanatan yankin tsakiyar jihar, wadda Lauya (barrister) David Umaru na jam’iyyar APC ya ci. Wakilinmu na jihar ta Naija Murtala Nasiru Batsari ya ruwaito baturen zabe Furfesa Ali Audu Jigam na bayyana cewa dan takarar na APC ne ya ci.

Baturen zaben ya ce David Umaru ya ci kuri’u 257,831 yayin da shi kuma Gwamna Aliyu ya ci 82, 094. Don haka ya ce dayake David Umaru ya cika dukkannin ka’idoji shari’a, “A nan an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.” Hukumar zaben jihar ta Naija ta kuma ba da sanarwar soke zabe a wurare 8 a wasu kananan hukumomi saboda matsalar satar akwatunan zabe in ji jami’in hulda da jama’a na hukumar zaben Madaki Muhammad Wasi.

Wakilinmu ya ce a daidai lokacin hada wannan rahoton daga kananan hukumomi 19 ne cikin jimlar kananan hukumomi 25 da ke jihar aka samu sakamakomnsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG