A Najeriya, rundunar 'Yansanda Ta jihar Taraba, ta kama mutum daya cikin gungun wadanda suke sayen katunan zabe daga hanun jama'a, bisa alkawarin cewa zasu sama musu ayyukan yi, ko rance daga hanun bankuna, wadanda ba'a bayyana sunayensu ba.
Wadanda lamarin ya shafa sun gayawa wakilin Sashen Hausa a yankin Ibrahim Abdulaziz cewa, mutumin ya karbi katunan zabe daga hanun mutane fiye da 50 wadanda aka sani a yankin na Tela.
Kama wanda ake zargin Alhaji Habu Iliya, ya taimaka wajen bankado gungun irinsu wadanda suke bi suna sayen kantuna zaben mutane.
Da yake tabbatar da batun kakakin rundunar 'Yansanda a jihar Emmanuel Kwaji, yayi kira ga jama'a su bude ido kuma sai karar duk wanda ya tuntubesu da neman raba su da katunan zabensu.
Kwaji, wanda aka kaman ya yiwa wadanda ya karbi katunansu alkwarin sama musu ayyukan yi a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya.
Wani dan siyasa shugaban jam'iyyar hamayya a jihar yace har sarakuna da iayyen ma'aikata ake yiwa barazana cewa ko su yiwa PDP aiki ko akan aikinsu ko na wani nasu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5