Zabe: Za A Rufe Jami’o’in Najeriya Ranar 22 Ga Watan Fabrairu

Daya daga cikin dakunan taro a Jami'ar Bayero da ke Kanon Najeriya

Hukumar NUC da ke kula da jami’o’in Najeriya ta ba shugabannin jami’o’in kasar umurnin su rufe sai bayan zabe.

Wata wasika da hukumar ta aikewa shugabannin jami’o’in, ta nuna cewa Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya ba da umurni rufe makarantun don a ba dalibai damar yin zabe.

Umurnin ya yi nuni da cewa, jami’o’in za sa rufe daga ranar 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris.

A ranar 25 ga watan Fabrairu Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

A kuma ranar 11 ga watan Maris za a gudanar da na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.

“Duba da damuwa da aka nun akan kare lafiyar malamai da ma’aikatan jami’a da kuma dalibai, Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya ba da umurnin cewa a rufe dukkan jami’o’I da sauran harkokin karatu tsakanin 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watahn Maris.” Wani sashe na wasikar ya ce.