Kungiyoyin da suka haɗa da kungiyar malaman jami'ar Ghana (UTAG), da kungiyar masu gudanarwa ta jami'o'i ta Ghana (GAUA), da kungiyar ma'aikatan ilimi ta Ghana (TEWU-GH), da kungiyar manyan ma'aikata na Jami'o'in Ghana (SSA-UoG) sun bukaci gwamnati ta biya su kudin alawus na koyarwar da suka yi ta yanar gizo da ake kira OTSA a takaice, da kuma sauran wasu kudaden.
Kungiyoyin sun kuma bai wa masu daukar ma’aikata aiki gargadi da su dauki wannan maganar da muhimmanci domin baza su so su kawo cikas a kalandar ilimi ba.
"Kamata yayi kugiyar daukar ma’aikata aiki su gaggauta janye aniyarsa ta sake yanayin aikin malamai, idan ba haka ba fannin koyarwa da ayyukan da suka shafi dukkan cibiyoyin ilimi zasu tsunduma yajin aiki tun daga ranar Laraba 5 ga watan Oktoba na shekarar 2022," a cewar sanarwar da kungiyoyin suka fitar.
Ferfesa Solomon Nunoo, shugaban kungiyar UTAG, ya ce kungiyarsa da sauran wasu suna kashedi ga hukumar da ke da alhakin daukar ma'aikata da su kaucewa jefa karatun jami'o’i cikin mawuyacin hali, saboda kungiyar kwadago ba zata taba yadda da irin wannan rashin kula da yadda ake gudanar da aiki ba.
Shi kuwa Ferfesa Ransford Gyampo, malami kuma mamba a kungiyar UTAG, ya yi kira ga ministocin Ilimi, kudi, ayyuka, da shugaban kungiyar kwadago ta kasa, yana mai cewa suna iya yin watsi da bukatunsu, amma su sani cewa yajin aikin da zasu yi wannan karon zai zama wanda ba a taba ganin irinsa ba a fadin Ghana.
Shi ma malamin jami'a Siiba Shakibu Salisu, kuma mai Sharhi akan ilimi, ya ce yajin aikin zai iya gurgunta karatun dalibai. Don haka ya kamata gwamnati ta duba batun da sauri.
Hukumomin Ghana dai basu ce uffan ba akan batun.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim: