Kungiyar ‘Yan Najeriya Ta Zabi Sabbin Shugabanni a Jamhuriyar Nijar

Zaben Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Jamhuriyar Nijar

‘Yan Najeriya mazauna Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zaben mutanen da za su jagoranci kungiyarsu a ci gaba da kara inganta matakan samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasar a duk inda suke.

‘Yan Najeriya sun hallara a dakin taro na ofishin jakadancin Najeriya a Nijar domin kada kuri’ar zaben sabbin shugabannin mambobin kungiyar.

Sakamakon zaben ya nuna cewa, Iliyasu Ukuten, dan asalin jihar Kogi, shi ya lashe zaben.

Ukuten ya roki Allah da ya ba shi damar gudanar da aikin da aka zabe shi akai.

Zaben Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Jamhuriyar Nijar

Haka zalika, shi ma mutumin da aka zaba a matsayin mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Gambo Ibrahim, ya tabbatar da cewa za su yi aiki tsakaninsu da Allah.

Ya kuma ya kira ga ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Nijar da su bi doka da oda.

Sai dai kuma wasu da suka yi cincirindo a kofar ofishin jakadancin Najeriya, da nufin kalubalantar zaben da suke ganin alamar magudi a tare da shi, sun hadu da fushin jami’an tsaro.

Najeriya ta hada kan iyaka da kasar ta Nijar, suna kuma da al'adu kusan iri daya baya ga harkokin cinikayya da zamantakewa da suke yi a tsakaninsu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar ‘Yan Najeriya Ta Zabi Sabbin Shugabanni a Jamhuriyar Nijar - 3'02"