Rahotanni daga jihar Niger a Najeriya na cewa an samu karancin masu kada kuri’u a jihar yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihar.
Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa a birnin jihar na Minna babu mutane da dama a rumfunan zabe amma kuma a yankunan karkara an dan samu mutane da dama.
“Misali kamar a karamar hukumar kwantagora, an samu mutane da suka fita da dama.” In ji wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari.
Game da batun wani malamain zabe da aka zarga da yin dangwale a wasu kuri’u, bayanai sun ce tuni mutumin aka mika shi ga hukumomin tsaro bayan da aka cafke shi.
“Wani mai sa ido ne na hukumar zabe na karamar hukumar Rijau shi ne aka kama shi da wasu kuri’u wanda yawansu ya kai bandir biyu duk kuma an dangwala su da jam’iyar PDP.” Wakilin Muryar Amurka ya ce.
Your browser doesn’t support HTML5