Za’a Gurfanar Da Duk Wani Jami’in Gwamnati Da Aka Samu Da Laifin Zarmiya Gaban Kotu

Jerin Sabbin Minstoci a Bikin Rantsar Dasu a Abuja

Umarnin da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya bawa ministan Shari’a Abubakar Malami, na cewa ya gudanar da bincike kan kowaye aka samu da laifin zarmiya a gwamnatinsa da alwashin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi gaban kotu.

Kai tsaye dai gwamnatin bata ambaci sunayen wadanda take son a bincikesu ba. sai dai labaran da suka cika kafafen labaru sune, samun sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawal, da cunkusa kudi a kwangilar raya Arewa maso yankin Gabas, da Majalisar Dattawa tayi kan binciken kudin nome ciyawar nan ta Kachalla kan kudi Naira Miliyan 270.

Mai taimakawa shugaban kan labaru mallam Garba Shehu, yace za’a duba zarge-zargen da akeyi kan wasu manyan jami’an gwamnati don tabbatar da gaskiyar lamarin, idan kuma an samu duk wani jami’i da laifin tabbas za’a gurfanar da shi gaban kotu.

A wani batun na bangaren yaki da cin hanci shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume, yace za’a sake gabatar da sunan Ibrahim Magu gaban Majalisar Dattawan don yiwuwar tantance shi, wannan kuwa ya biyo bayan ‘kin amincewa da Magu da Majalisar ta yi bisa rahotan tsaro da ya jawo masa akasi.

Yanzu haka dai abin jira a gani shine ko wadanda za’a tuhumar da kuma hukuncin da zai hau kansu. A zamanin baya dai anyi awon gaba da tsohon sufetan ‘yan sandan Najeriya Tafa Bolugun da kuma wani tsohon ministan ilimi Fabian Osuji kan zargin zarmiya.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Za’a Gurfanar Da Duk Wani Jami’in Gwamnati Da Aka Samu Da Laifin Zarmiya Gaban Kotu - 2'56"