Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Haram Ne Gwamnoni Su Dinga Nadawa Kananan Hukumomi Kantamomi - Kotun Koli


Farfasa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya ko INEC
Farfasa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya ko INEC

Tun lokacin da mulkin dimokradiya ya dawo Najeriya gwamnoni ke sauke shugabannin kananan hukumomi suna nada kantamomi ko shugabannin wucin gadi na watanni shida shida tamkar kananan hukumomin basu da 'yanci.

A karshen makon jiya bayan sauararen karar da shugabannin kananan hukumomi suka gabatar kan yadda gwamnan jihar Ekiti ya dakatar dasu domin ya nada kantamomi, kotun kolin Najeriya ta ayyana cewa haramun ne gwamnonin Najeriya su dinga nada kantoma ko shugaban riko na kowace karamar hukuma.

Kotun yace hakan ya ci karo da sashe na bakwai na kundun tsarin mulkin Najeriya. Haka ma Juma'ar da ta shude babar kotun jihar Kaduna ta haramta yunkurin da gwamna El-Rufai keyi na nada shugabannin riko a kananan hukumomin jihar ishirin da ukku bayanda wasu mutane suka kalubalanci yunkurin a gabanta.

A taro da manema labarai a Kano shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta Najeriya Kwamred Ibrahim Khalil yace suna cike da farin cikin abubuwan da suka faru kuma sun godewa fannin shari'a da ya fito karara ya fadi abun da kundun tsarin mulki ya fada.

Baicin fannin shari'a Kwamred Khalil ya godewa majalisun tarayya na jajircewa ganin kananan hukumomi sun samu nasu kason kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya.

Shi ma tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Rimin Gado wanda yanzu shi ne shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano Kwamred Muhimi Magaji wanda yayi nasara a babbar Kotun jihar Kano a shekara ta 2010 bayan da ya kalubalanci gwamnatin Kano na nada kantamomi wa kananan hukumomi yace hukumcin na kotun koli ya kara gaskatashi. Yace kotun koli ta fito da gaskiyar abun da suke fadi.

Saidai Kwamred Khalil yace muddin hukumomin zaben jihohi ne zasu gudanar da zaben kananan hukumomi to dimokradiya ba zata tabbata a kananan hukumomin ba.

Amma Magaji yace tunda kundun tsarin mulki ya ba hukumomin zaben jiha su shirya zabukan su ne zasu yi kokarin kare mutuncinsu su tabbatar da adalci.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG