Wannan rikici ya jawo kwararar yan gudun hijira zuwa wasu garuruwan dake makwabtaka da yankin na Dan Anacha.
Bangarorin biyu na zargin juna da soma takalar rikicin,inda hadakar kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ke zargin sakaci da kuma shakulatin bangaren tsaro da cewa su suka jawo wannan tashin hankalin da yanzu haka ma ya raba daruruwa da gidajensu .
To sai dai kuma yayin da hankula ke kwantawa, kungiyar ta Miyetti Allah ta bukaci da a hanzarta kafa kwamitin bincike,inda ta yi zargin cewa ya zuwa yanzu akwai wasu makiyayan da ba’a san halin da suke ciki ba,kamar yadda Alhaji Mafindi Danburam dake cikin shugabanin kungiyar Miyetti Allah a shiyar arewa maso gabas ya tabbatar.
Koda yake shima da yake tsokaci kan wannan tashin hankali, daya daga cikin shugabanin yan kabilar Tibi a yankin Onarebul Doiro Manyan ya bukaci hukumomin gwamnatin jihar Taraban,da su dau mataki tare da tallafawa wadanda ke gudun hijira sakamakon wannan rikici.
A nata bangaren,rundunar 'yansanda jihar Taraba, ta bakin kakakinta ASP David Misal tace hankula sun kwanta biyo bayan karin jami’an kwantar da tarzoman da aka tura yankin.
Dangane kuma da rahotannin da ke cewa mutanen yankin sun gudu, kuma rayuka20 suka hallaka ya ce ba haka ba ne .
Ko a watan Fabrairu ma irin wannan rikicin ya afku a jihar, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani