Sufeto janal na rundunar ‘yan sandan Najeriya Alhaji Ibrahim Idriss ne ya bayyana hakan a wajen bukin kaddamar da ginin sabon barikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da aka gudanar a garin Kwantagora na jahar Neja.
Alhaji Ibrahim Idriss, yace wannan Bariki na ‘yan sandan kwantar da tarzoma shine na 61 a duk fadin Najeriya, kuma bisa ga la’akari da yadda yankin na Kwantagora ke fama da masu aikata mugayen aiyuka, yasa suka dauki matakin bude sabuwar Barikin.
Gwamnatin jahar Neja ce ta dauki nauyin samar da fili da kuma gina Barikin. Kamar yadda gwamnan jahar Alhaji Abubakar Sani Bello, ke cewa samun zaman lafiya abu ne mai muhimmanci a fannin rayuwa da ci gaba, wanda in babu zaman lafiya duk abin da za a yi bata lokaci ne.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun nuna jin dadinsu ganin yadda aka gina sabon Barikin ‘yan sanda a garin Kwantagora, haka kuma suna ganin garuruwan dake zagaye da Jahar Neja da suka hada da Zamfara da Kebbi da Kwara da kuma Kogi, zasu amfana da wannan ci gaban da aka samu.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.