Sarakunan dai sun bayyana hakan ne a wajen wani taro da Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Canada suka shirya wa masu rike da sarautun a babban birinin tarayyar kasar Abuja kan yadda za a kawo karshen cin zarafin mata da ake yi a harkokin siyasa a fadin kasar.
Masu rike da sarautun gargajiyar da suka fito daga sassan kasar daban-daban kama daga arewaci da ma kudanci ne suka halarci taron da Majalisar Dinkin Duniyar da gwamnatin kasar Canada suka shirya.
Manufar taron dai shi ne fadakar da jama’a kan muhimmancin shigar mata cikin sha’anin siyasa da ba su dukkanin damammaki kamar yadda takwarorinsu maza ke samu,.
Sannan da kawo karshen irin muzgunawar da ake yi musu a harkar siyasa, abin da ke sanyaya wa mata da dama gwiwa wajen shiga siyasa duk kuwa da suna da ra’ayin ba da ta su gudunmawa a faggen na siyasa da shugabanci.
Mrs. Beatrice Eyong ita ce wakiliyar mata ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya da kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin nahiyar Afrika wato ECOWAS, ta kuma ce babbar manufar taron shi ne nusar da masu rike da masarautun gargajiya irin yadda muzgunawa mata yake mummunar illa ga ci gaban siyasa dama ci gaban kasar baki daya.
Ta kara da cewa jagororin masarautun na gargajiya sun nuna cewa a wasu lokutan mata ba sa karfafawa 'yan uwansu mata gwiwa, don haka ta yi kira ga mata 'yan uwanta da su rika karfafawa juna gwiwa ta hanyar jefa mu su kuri’a a lokutan zabe.
Daga manyan sarakunan da suka halarci taron akwai basaraken jihar Neja wato Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar wanda ya tabbatar da cewa mata ba sa samun irin wannan damar, yana mai cewa a matsayinsu na iyayen al’umma za su fadakar da jama’a kan muhimmacin shigar mata al’amuran siyasa.
A nasa bangaren, mai martaba sarkin Fika daga jihar Yobe, Muhammad Abali Ibn Muhammad Idrissa, ya ce la’akari da irin tasirin da suke da shi a cikin al’umma da kusancinsu da jama’a, za su ci gaba da fadakarwa don a bar mata su taka rawar da ta dace da su a siyasance.
Da alama dai jami’an na Majalisar Dinkin Duniya da suka shirya taron na cike da fatan cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu kamar yadda babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya, Matthias Schmale, ya bayyana cewa kalaman sarakunan gargajiyar sun karfafa musu gwiwa.
Wasu mutanen na cewa sarakunan gargajiya su ne ke rike da al’adun jama’a tare da nuna yakinin cewa za su taka muhimmiyar rawa wajen sauya tunanin jama’a da dabi’un da ya kamata a sauya. Kuma abu ne mai karfafa gwiwa ganin yadda suke kallon irin rawar da ya kamata su taka a aikin kawar na kalubalen da mata ke fuskanta wajen taka rawa a al’amuran jama’a.
A yanzu dai da yake an kammala zabuka fidda gwani, mai yiwuwa abin da sarakunan za su mayar da hankali a kai shi ne neman goyawa matan da suka fito takara samun nasara, da kuma tabbatar da cewa mata sun samu damar kada kuri’unsu ba tare da wata fargaba ko barazana ba.