Idan kuna biye da mu, shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin wadansu ‘yan siyasa da su ka hada da mata da suka tsaya takara, wadanda ke nazarin yadda mata za su iya taimakawa ‘yan’uwansu da jam’iyunsu su ka tsayar takara, su iya kai ga nasara a zaben da ke tafe a Najeriya.
Bakin dai su ne. Hajiya Khadija Abdullahi Iya ‘yan takarar gwamnan jihar Naija ta jam’iyar AFGA, da Mrs Dorathy Nuhu Aken ‘Ova wadda ta nemi a tsaida ita takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar SDP, sai kuma Hajiya Mariya Ibrahim Baba ‘yar siyasa kuma ‘yar gwaggwarmaya, da kuma dan siyasa Sa’idu Gombe.
Hon Sa’idu Gombe na bayanin kan inda yake ganin rauni a siyasar mata lokaci ya kwace mana, inda kuma mu ka dora ke nan yau a tattaunawar da Shamsiya Hamza Ibrahim ta jagoranta:
Saurari cikakken shirin cikin sauti: