Wannan ne karon farko tun bayan zaben wakilin mazabar Zariya, Hon. Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalissar wakilai da ya debo tawagar 'yan-majalissun tarayya da na jihohi don zuwa fadar mai-martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad a wata ziyara.
Tajuddeen wanda shi ma ya na da mukami na Iyan Zazzau a masarautar, ya ce za su yi duk mai yiwuwa don ganin sarakuna sun sami gurbi a kundin tsarin Mulkin Najeriya.
Dama dai mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya nunawa sabon shugaban majalissar wakilan damuwar sarakuna ne kan yadda aka dinga dankwafe kokarin ganin an sama musu gurbi a kundin tsarin Mulkin Najeriya.
Mataimakin shugaban marasa Rijaye Hon. Aliyu Sani Madaki na cikin tawagar shugaban majalissar wakilan a fadar Sarkin Zazzau, kuma ya ce za su ba da gudummawar tabbatar da wannan kuduri.
Shi ma shugaban majalisar dokokin Jahar Kaduna, Hon. Yusuf Liman na goyon bayan baiwa sarakuna dama.
Yunkurin saka sarakuna cikin sha'anin mulki a kundin tsarin Mulkin Najeriya dai ya dade yana yawo a majalisu kuma bai taba tsallake dukkan matakai ba ballanta ya kai ga shugaban Kasa.
To shin ko wannan karon kudurin dokar zai kai labari, tun da 'yan majalisar da kan su ke son kai shi? Lokaci kadai ka iya amsa wannan tambaya.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5