Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KOGI: Ana Binciken Wasu Manyan Sarakuna 2 Kan Rikicin Kabilanci


Taron kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasa
Taron kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasa

Gwamnatin jihar Kogi tace tana gudanar da bincike akan wasu manyan sarakunan jihar guda 2, game da wani mummunan tashin hankalin da yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 9 tare da kona gidaje da dama a 'yan kwanakin da suka gabata a karamar hukumar Bassa dake cikin jihar Kogin.

Rahotanni dai sun nuna cewa manyan sarakunan guda 2 masu daraja ta daya da sun hada da Alh. Khalid Ali Bukar Sarkin Mozum, da Agumo of Bassa wato Sarkin Bassa, da kuma Chif William Keke dukansu a yanzu haka suna hannun hukumomi a jihar Kogin domin gudanar da bincike akan lamarin.

Gwamnatin jihar Kogin dai tace yankin na Bassa ya dade yana fama da tashin hankali da ya shafi kabilanci da kuma rikicin mallakar filaye a tsakanin 'yan kabilar Egbira da kuma Bassa komo.

Al’amarin da Gwamnatin Jihar Kogin ke gani sarakunan na da rawar takawa wajan shawo kan wannan matsala kamar yadda kwamishinan labarai na jihar Kogin Mr. Kinsley Fanwo yayi karin bayani, inda yace bawai an kama su bane, an gayyace su ne domin suyi karin haske akan matsaloli da dama da za su taimaka wajan dorewar zaman lafiya a wannan karamar hukuma ta Bassa.

Kwamishina Fanwo yace gwamnati tayi kokarin dawo da zaman lafiya a wannan yanki, kuma akwai wani tsari da aka samar da zai hana aukuwar abinda ya faru a baya.

Daya daga cikin sarakuna yankin da aka kona gidansa sakamakon tashin hankalin na kwanakin baya da a yanzu haka ya ke gudun hijira, wato Hakimin Mozum, Alh. Haruna Abubakar, yace duk da suna gudun hijira, a yanzu haka suna kokarin karbar Belin Babban sarkin nasu.

Masu sharhi akan lamurran tsaro dai na ganin matakin rike manyan sarakunan yankin guda 2, watakila ya taimaka wajan gano bakin zaren da zai taimaka wajan shawo kan matsalar tashin tashina da a aka dade ana fama da ita a wannan yanki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG