To sai dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana nazarin kalaman da ‘yan siyasa ke yi masu tayar da husuma kuma zata yi dirar mikiya kan wadanda ta samu da hannu ga munanan kalaman.
Yadda aka gudanar da zabubukan shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin tarayyar Najeriya, baya rasa nasaba da abin da ke ci gaba da tunzura wasu ‘yan siyasa suna furta kalamai munana wadanda ke iya tayar da fitina a zaben da ke tafe na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Alalmisali irin yadda rundunar 'yan sanda ta ayyana neman dan majalisar dokoki na mazabar cikin garin Bauchi, ruwa a jallo, akan zargin hada baki da tayar da fitina, manuniya ce ga yadda ‘yan siyasa ke rura wutar fitina duk da hannunka mai sanda da ake yi musu.
A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar, tun kafin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya zaunar da ‘yan takarar gwamna wuri daya ya ja musu kunne, an samu wasu munanan kalamai da ‘yan siyasa suka furta wadanda har yanzu suna zagayawa a shafukan sadarwar yanar gizo, wasu daga cikin su manyan ‘yan siyasa ne suka furta su.
Duk da yake irin wadannan kalaman suna da yawa kuma dukan jam'iyun APC da PDP sun furta su, wanda ya fi daukar hankalin jama'a shi ne wanda ake cewa, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Tambuwal ya furta, kuma akan haka na tuntunbi jagororin jam’iyyar inda kakakinta Sambo Bello Danchadi ke cewa, kalaman sun samu asali ne daga kalaman da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi. Ya ce kamata ya yi shugabanni su rika auna maganganun da suke yi domin ayi koyi da su.
Magoya bayan jam'iyyar PDP ma sun furta kalamai da ke iya tunzura jama'a kamar wadanda ake cewa gwamna da kansa ya furta, sai dai da na tuntubi kakakin jam'iyar Hassan Sahabi Sanyunnawal ya ce kalaman gwamna ba na batanci ba ne, kuma tamkar a tauna tsakuwa ne a bai wa aya tsoro.
Jami'an tsaro sun ce suna daukar matakai domin kar karamar magana ta zama babba, da yake kwanakki kadan suka rage ga zabubukan gwamna da ‘yan majalisar jiha.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Sakkwato, Muhammad Usaini Gumel, ya ce bisa ga umurnin babban Sufeto na kasa, basu kama wadanda ake tuhuma, sai in sun samu kwararan shaida ga abin da ake tuhumar su akai.
Ya ce yanzu suna nazari akan kalaman tunzura jama'a da wasu ‘yan siyasa suka furta kuma da zarar sun samu kwararan shaida za su kama su, su gurfanar da su gaban kuliya.
Mai sharhi akan lamurran yau da kullum Farfesa Bello Badah y ace abin da ya kamata ayi don kwantar da wadannan kalamai da ke iya zama barazana lokutan zabubuka shi ne a nemo wadanda suka yi kalaman su warware kalaman, su kuma yi da'awar zaman lafiya, ko kuma shugabanni su fitar da bayanai masu kwantar da hankalin jama'a.
Ko bayan fadakarwa da shugabannin al'umma ke yi malaman addini ma sun dukufa ga jan hankulan ‘yan siyasa domin kauce wa duk abin da kan iya tayar da husuma a lokutan zabubuka, da ma bayana zabubukan.
Saurari cikikken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5