Daya daga cikin ababen dake saurin harzuka jama’a, musamman mabiya addinai shine yin kalamai game da addini, wanda kuma shine wassu ‘yan siyasa ke amfani da shi don rarraba kan jama’a da zummar cimma burinsu.
Jahar Nasarawa dake da tarihin zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, a wannan kakar zaben, an fara samun cecekuce dake rura wutar rikicin da in ba’a sha kanta ba, zata zame matsala.
Shugaban kungiyar hadin kan Kirista a Jahar Nasarawa, Veri Rabaran Fada, Sunday Emma ya ce basu bukatar wani yanayi da zai bata zamanta kewarsu.
Shima sakataren kungiyar JNI a Jahar Nasarawa, Imam Muhammad Ali ya ce suna kan fadakarwa kan zaman lafiya.
Gwamnan jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a jahar ya ce al’ummar jahar Nasarawa na zaune lafiya da junanasu dake da bambancin addinai.
A jahar Filato ma, an sami irin wadannan cecekuce, wanda ‘dan takarar gwamna a jami’iyyar PDP, Barista Caleb Mutfwang ya roki jama’a su kwantar da hankulansu.
A shekarun baya dai irin wadannan kalamai marasa dadi sun haddasa munanan rikicin bayan zabe, da ya kai ga rasa rayukan jama’a da salwantar dukiyoyi masu tarin yawa.
Ga dai sautin rahoton Zainab Babaji daga birnin Jos: