Kan haka ne kungiyar Fulani ta Jonde Jam ta gudanar da taronta na kasa a Jos, fadar jahar Pilato inda ta hado kan matasa daga dukkan sassan Najeriya domin tattauna tsare-tsaren da zasu bullo da shi don samar da zaman lafiya a Najeriya.
Shugaban kungiyar, Alhaji Saidu Maikano, ya ce sun shirya wannan taro don kaddamar da shugabannin kungiyar na jihohi a duk fadin kasar kuma aikin da zasu yi shi ne za su bi gida-gida da ruga-ruga don wayar da kan fulani.
Ya ce wannan kungiya babu cuta ba cutarwa kuma da yadda Allah za a samu mafita a wannan kasar, sannan ya bada shawara ga dukkan baza gurbi ba a matasan fulani ba a dukkan sauran kabilun Najeriya da su gyara halayen su kuma su san addinin su.
Ita ma Shugabar mata ta kungiyar Jonde Jam, Aminatu Saidu daga jahar Taraba ta ce duk abin da mutum ya ke yi idan babu ilimi babu abin da zaka iya yiwa al’ummarka, dole sai da ilimi, kuma duniya siyasa ce saboda haka suna shiga kauyuka su gayawa iyaye mata da yara kuma su ga yadda suke karatu su fadarkar da su.
Ta kuma kara da cewa suna kiran mata su gyara halayensu kuma su gayawa mazajansu idan suka tafi neman abinci su rinka kawo musu halal domin duk abin da mutum ya yi gaskiya sai an tambaye shi kuma kada su rinka yi aikin da ba su san hukuncin sa ba.
Shima a hirarsa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, shugaban kungiyar Miyyati Allah ta kasa reshen jihar Filato, Abdullahi Idris Bayero, ya ce mai laifi mai laifi ne abin da basa so a Najeriya shi ne yadda aka ayyana bafulatani kawai idan an ganshi an ga mai laifi, bai kamata ba.
Ya yi kira ga fulani duk wani mai laifi ko bafulatani ne a fito a kama shi kana ya bada shawara ga fulani da su kama sana’a kuma su sa tsoron Allah da kishin Najeriya a zuciyarsu. Ya kuma yi kira ga Fulani cewa, "idan akwai wani mai laifi ko bafulatani ne dan uwanka ko uwa daya uba daya ku fadarkar da shi kuma a gayawa ‘yan sanda don idan ka bar shi to ba zai barka ba."
A lokacin da yake jawabi a wurin taron, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan a bangaren gudanarwa a jihar Filato, Aliyu Sale Tafida, ya shawarci mahalarta taron cewa, duk inda su ka ga mai laifi su fidda shi. ya kuma yi kira garesu su hada kai su zama tsintsiya madaurinki daya, su kuma hada kai su kawo wa ‘yan sanda labari.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5