Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba da umurni da a janye dukkanin ‘yan sandan da ke bai wa masu rike da mukaman siyasa tsaro da wasu fitattun mutane.
Idris ya ba da umurnin ne a yau Litinin,a wani taron Kwamishinonin ‘yan sandan kasar da aka yi a Abuja, babban birnin kasar.
“Umurnin janye dukkanin jami’an ‘yan sanda da ke tsaron fitattun mutane, da ‘yan siyasa masu rike da mukamai da kuma masu rike da ofisoshin yi wa al’uma hidima, zai fara aiki ne nan take.” Inji Idris.
Daga cikin ire-iren mutanen da har ila yau wannan mataki zai shafa, akwai ‘yan kasuwa, kamfanoni masu zaman kansu da kuma attajirai.
Ya kara da cewa daukan wannan mataki ya zama dole, lura da yadda Najeriya ke fuskantar matsalar tsaro, yana mai cewa hakan zai ba da damar a sa ido kan harkokin tsaron kasa.
Shugaban ‘yan sanda na Najeriya, ya kara da cewa, za a aikawa da shugaba Buhari wasika domin neman amincewarsa da daukan wannan mataki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Idris ya ba da umurnin a daidaita tare da yin garanbawul ga tsarin na bai wa 'yan siyasan da kuma ma'aikatan gwamnatin kariya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin jin cikakken bayani:
Your browser doesn’t support HTML5