Gwamnatin jihar ta shirya wani taro na masu ruwa da tsaki a yankin Mambila, don sasanta al’umomin da basa ga maciji da juna.
Taron na daga cikin matakin da hukumomin tsaro a jihar Taraba ke dauka ayanzu, na dawo da doka da oda a wasu yankunan dake fama da tashe tashen hankula na kabilanci da na addini, musamman yankin Mambilla inda aka samu asarar rayukan jama’a da dama baya ga na dabbobi cikin kwanakin nan.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsakin a tsaunin Mambilla, mataimakin gwamnan jihar Taraba Haruna Manu, ya ce yanzu gwamnatin jihar a shirye take wajen nemo bakin zaren magance tashe tashen hankulan dake faruwa, to amma kuma ya ce haka ba zata cimma ruwa ba muddin al’ummomin da lamarin ya shafa basu shirya sasantawa ba.
Shima da yake tsokaci a madadin shugabanin hukumomin tsaro a jihar, daraktan hukumar tsaro ta DSS, a jihar Taraba, Alhaji Shehu Saulawa, ya gargadi al’ummomin dake boye makamai da su su mika makamansu don gudun fadawa hannun jami’an tsaro.
Ko bayan zuwan shugaba Buhari jihar Taraba, sai da aka sake samun tashe tashen hankula a yankin na Mambilla, dake albarkatun kasa da wurin kiwo, lamarin da ya jawo asarar rayuka wanda kuma wasu lokuta akan danganta lamarin da rikicin fili, kamar yadda wasu yan yankin ke cewa.
Ya zuwa yanzu ‘kura ta fara kwantawa, to amma kuma akwai jama’a da dama dake gudun hijira batun da manazarta ke ganin dole a tashi tsaye.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum