Farfesa Osinbajo, ya ce don tabbatar da an kare makarantu daga irin harin da mayakan Boko Haram suka kai garin Dapchi, shugaba Mohmmadu Buhari ya damu da matsalar tsaro musamman da ake fuskanta a halin yanzu.
Inda shugaban ya sha nanata cewa suna sane da cewa talakawa ne suka zabe su musamman a wancan lokaci bisa yadda matsalar tsaro ta addabi Najeriyar, saboda haka za a yi duk mai yiwuwa don ganin an shawo kan wannan al’amari.
Ganin yadda satar ‘yan matan Dapchi ta tayar da hankulan ‘yan Najeriya, kwararru irinsu Malam Ibrahim Mohammad Damaturu, na cewa kamata ya yi a dauki darasi tun lokacin da aka sace ‘yan matan Chibok, don tabbatar da cewa irin hakan bai sake faruwa ba.
Masanin tsaro, Kwamanda Musa Isa Salmanu, na ganin cewa dole ne jami’an tsaro su kara tashi tsaye kan abubuwan da suke a baya, ta hanyar tattara bayanan sirri da amfani da su.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum