Baban bankin Masar yace za’a rufe cibiyoyin kudi a duk fadin kasar a yau litinin da kuma gobe Talata saboda bikin Maulidi da kuma yajin aiki. A yau litinin wata kafar soja tace rundunar soja tana shirye shiryen haramta yin yajin aiki, kuma tayi kashedin cewa zata dauki mataki akan duk wanda ke kokarin karya doka ko jawo rudami. A jiya lahadi rundunar soja ta rushe Majalisar wakilai kuma ta dakatar da amfani da tsarin mulkin kasar, biyu daga cikin muhimman bukatun masu zanga zangar neman mulkin democradiya, kwanaki goma sha takwas bayan boren da ya hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak. A jiya lahadi rundunar soja ta gabatar da sanarwar cewa zata ja ragamar mulkin wucin gadi ta tsawon watani shidda ko kuma har lokacinda aka gudanar da zaben shugaban kasa dana wakilan Majalisar wakilai. An dai shirya gudanar da zabubbukan a watan satumba idan Allah ya kaimu. Baya ga haka kuma shugabanin soja sunyi kokarin daidaita al’amurra a birnin Alkahira a jiya lahadi, yayinda suka tura sojojin da suka kware tantunan da masu begen mulkin democradiya suka kakkafa a dandalin Tahrir domin zirga zirgan motoci su koma kamar da. A wani wuri dabam a birnin Alkahira kuma, a jiya lahadi daruruwan yan sanda suka yi zanga zangar a harabar ma’aikatar harkokin cikin gida dake kula da harkokinsu suna bukatar karin albashi da kuma bukatar a ladaptar da jami’an da suka yi zargin cewa sun bata musu suna. Sojojin dake gadin ma’aikatar sunyi harbin gargadi tare kuma da baiwa hamata iska da wasu yan sandan domin hana su shiga ma’aikatar. ‘Yan sandan Masar sunyi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa a karkashin shugabancin Mubarak.
Baban bankin Masar yace za’a rufe cibiyoyin kudi a duk fadin kasar a yau litinin da kuma gobe Talata