Sabbin shugabannin mulkin soja a Masar suna kira da a kawo karshen jerin yajin aiki da suka barke ta ko ina fadin Masar mai gurgunta lamura,wadda ya biyo bayan juyin juya halin da aka yi,sun nuna alamun zasu yi aiki tare da farar hula,kuma zasu yi wa tsarin mulkin kasar garambawul ta kuri’ar raba gardama.
Majalisar kolin mulkin sojar a sakamakon bayan taro da ta bayyana jiya litinin,ta yi kira ga kungiyoyin kwadago su kawo karshen yajin aikin,suna gargadin cewa yajin ayyukan da ake yi suna iya barazana ga tattalin arzikin kasar dake neman farfadowa daga zanga zangar gama gari na mako biyu da aka yi.
Abinda kawai ya rage basu fada ba shine haramata yajin aiki da wasu nau’in zanga zanga,a yayinda kuma ta yi kokarin tabbatarwa ‘yan hamayya cewa da gaske take gameda tsara shirin mika mulki.
Cikin fitattun kungiyoyi da suka shiga yajin aiki gadan gadan ko ‘yar kwariya kwariya,har da ‘yansanda,ma’iakatan masaku,leburori,ma’aikatan Bankunan gwamnati da na kananan hukumomi,ma’aikatan hakar mai da na iskar gas,da kuma direbobin motocin kiya kiya.Ma’aikata sun bayyana dalilansu na yajin aiki da suka hada d a cinhanci da rashawa da kuma neman Karin alabshi.
Jiya litinin hadakar kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya matasa da suka taka muhimmiyar rawa wajen shirya zanga zangogin da suka kai ga hambare shugaba Hosni Mubarak sun gabatar da bukatar sun a neman ganin an fara shirye shiryen maida mulki hanun farar hula.
Kungiyar juyin juya halin matasan ta ayyana wa’adin kwana 30 na ganin an kafa gwamnatin farar hula da masana da zata maye gwamnatin wucin gadin da tsohuwar gwamnatin Hosni Mubaraka ta kafa,bayan barkewar zanga zanga a kasar ranar 25 ga watan jiya.
Ahalin yanzu kuma,Masar ta gabatarwa Amurka da Tarayyar Turai bukatar aza takunkumi kan dukiya da kadarorin wasu daga cikin manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Hosni Mubarak.
Jami’an Amurka da na Tarayyar Turai basu bayyana sunayen wadanda aka ambata cikin bukatar ba,sai dai babu sunan Hosni Mubarak ciki.