A jiya lahadi kasar Chadi ta gudanar da zaben Majalisar wakilai a karon farko cikin shekaru tara. Masu zabe sun fuskanci zabi tsakanin jam’iyar Patriotic Salvation Movement wadda take da rinjaye sosai a Majalisar wakilai da kuma yan takarar kawancen jam’iyun masu hamaiya ta CPDC. Shugaban tawagar wakilan kungiyar kasashen turai dake lura da zaben Louis Michel yace wasu rumfunan zabe sunyi makarar sa’o’i biyu wajen budewa. To amma kuma yace tawagarsa bata ga wasu kurakuran da aka yi da nufin yin magudi ba. Shugaba Idris Derby wanda ya kada kuri’arsa a birnin Njamena yace zaben wani muhimmin mataki na kafa mulkin democradiya a Chadi. Jam’iyun masu hamaiya sun kauracewa zaben da aka yi a shekara ta dubu biyu da shidda, zaben da shugaba Derby ya lashe. A shekara ta dubu biyu da bakwai masu hamaiya suka rattaba hanu akan wata yarjejeniyar data share fagen zaben da aka yi jiya lahadi.
A jiya lahadi kasar Chadi ta gudanar da zaben Majalisar wakilai a karon farko cikin shekaru tara.