Za'a Gurfanar Da Malaman Makarantar Islamiya Ta Rigasa a Gaban Kotu

Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna ta ce ta kammala bincike kan makarantar nan ta Rigasa wadda aka ga yara a daure kuma za ta gurfanar da malaman makarantar a gaban kotu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo Abubakar, ya ce duk da yake gwamnati ta damka yaran makarantar ga iyayensu, akwai yiwuwar gayyato wasu iyayen gaba kotu.

DSP Sabo ya kuma kara da cewa duk iyayen da suka nuna suna sane da azabtar da yaransu a makarantar za’a tuhume su da laifi, amma wadanda ba su san abun da ke faruwa ba sai dai su ba da sheda gaban kotu.

Ita ma kwamishinar harkokin mata da walwalar al'uma ta jahar Kaduna, Hajia Hafsat Mohammed Baba, ta ce gwamnati ta dauki damarar bincike inda tuni aka rufe makarantar.

Shi ma babban daraktan hukumar kula da harkokin addini a jahar Kaduna, Sheik Mohammad Jamilu Abubakar Albani, ya ce gwamnati na da tsari kan makarantun addini amma za ta kara tsaurara wadannan matakai.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Gurfanar Da Malaman Makarantar Islamiya Ta Rigasa Gaban Kuliya