A Najeriya, wata kungiya mai ayyukan habbaka kula da lafiyar mata masu juna biyu da ake kira Breakthrough Action Nigeria dake samun tallafin kungiyar bada tallafi ta kasar Amurka wato USAID sun kafa wani kwamitin malaman addinai da kuma iyayen kasa a jihar Bauchi da suka koya musu dabarun ilmantar da al’umma muhimmancin sauya munanan dabi’u dake kawo nakasu ga mata masu juna biyu da kuma yara kanana.
Ayyukan kwamitin sun hada da ziyartar kananan hukumomin jihar domin ganawa kai tsaye da al’umma da kuma kai ziyara asibitoci a ranakun da mata masu juna biyu ke zuwa ganin likita domin gabatar da bayanai kan muhimmancin kulawa da mata da yara.
Malama Hadiza Jibril Ahmed, ita ce jami’ar kungiyar Breakthrough Action, ta yi karin haske dangane da muhimmancin sanya malaman addinai a shirin.
Alhaji Abdullahi Yakubu marafan Bauchi, shi ne shugaban kwamitin da zai gudanar da shirin wayar da kan al’umma.
Facebook Forum