JIhar Yobe Zata Ranto Kudi Samada Naira Bilyan Daya.

Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Yobe.

Tuni majalisar dokokin jihar ta amince da wannan bukta da bangaren zartaswa ta aike mata.

Majalisar dokokin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, daya daga cikin jihohi da suke fuskantar matsalolin tsaro daga kungiyar Boko Haram, ta amince da bukatar da gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ya gabatar mata, na neman izinin ya ranto kudi Naira milyan dubu daya da milyan dari hudu.

Kamar yadda shugaban masu rinajye na majalisar Alhaji Usman Adamu yayi bayani, yace gwamnati zata yi amfani da kudaden ne wajen sake farfado da makarantun da suka lalace sakamakon hare haren Boko Haram, da cibiyoyin kiwon lafiya, da wasu kayan more rayuwa.

Gameda ko ana iya karkata kudaden nan domin yakein neman zabe mai zuwa, sanin gwamnan jihar zai sake bayyana kudurinsa na sake takarar kujerar gwamnan jihar ranar Asabar mai zuwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yobe Zata karbo Bashi