Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Mutane na Karo da Juna Akan Janaral Buhari


Mohamed Abrini, l'un des principaux suspects des attentats de Paris, 24 novembre 2015
Mohamed Abrini, l'un des principaux suspects des attentats de Paris, 24 novembre 2015

Tunda Janaral Buhari ya bayyana aniyarsa na tsayawa zaben shekarar 2015 aka soma samun sabanin ra'ayi akan cancantar tsayawarsa ko rashin hakan.

Shaikh Dr Gumi yana cikin wadanda suka fito karara suka umurci Janaral Buhari da kada ya tsaya takarar shugaban kasa. Maimakon yin hakan kamata yayi ya koma gefe daya ya zama uba.

Kalamun irin su Dr Gumi sun jawo ra'ayoyi daban daban. Wani yace shawarar da Dr Gumi ya bayar tayi daidai idan aka yi la'akari da abubuwan da suka faru a baya can da kuma abun da suke hange gaba.

Haruna Ahmad Danmaliki yayi watsi da shawarar Dr Gumi domin har yanzu talakawa na son ya tsaya sai hakonsa ya cimma ruwa. Yace maganar Dr Gumi tamkar akwai lauje cikin nadi. Yana ganin makudan kudi aka dankawa Dr Gumi domin ya fadi maganar.

Wani yace idan Buhari bai yi takara ba to babu adawa mai karfi a kasar. Yace bai kamata ya bari ba domin sauran 'yan takarar wato Kwankwaso da Atiku duk daga PDP suka fito. Idan Janaral Buhari bai tsaya ba to ya barwa PDP ke nan.

A cewar wani furucin Dr. Gumi bai dace da malaman addini ba. Idan aka cire Buhari babu wanda zai iya ceto kasar daga irin bala'in da ta shiga kamar talauci da rashin tsaro. Maganar siyasa bata malaman addini ba ce.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG