Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan APC a Yobe Na Korafi


Masu ruwa da tsaki a siyasar Jihar Yobe, daga shiyya ta uku ta mazabar ‘yan majalisar dattijai, sun koka ga irin saniyar ware da ake nuna musu a siyasar Jihar Yobe.

Mai magana da yawun wannan ayari dake bayyana wannan koke shine Alhaji Muhammadu Gaskanta yace tun lokacin da demokradiyya ta koma Najeriya a 1999, shiyya ta 1 da ta 2 ne ke bada gwamna da mataimaki, amma shiyyarsu ta uku basu taba samun wannan gata ba.

“Abunda yake tafe da mu, albishir ne mai kyau. Da farko mun nemi alfarmar a bar mana wannan takara kamar yadda aka yi shekara 16. Wannan shugabanci na Jihar Yobe, tsakanin Zone A da Zone B yake zuwa. Mu zone C bamu taba yi ba” a cewar Alhaji Gaskanta.

Mr. Gaskanta ya kara da cewa an hanna mutan ‘yankinshi siyar takardar tsayawa takara, inda yace zasu dauki mataki akan hakan.

“Wannan maganganu da mukeyi na daga cikin abunda zai jawo hankulan jama’a su fahimci irin matsalar mu.”

Alhaji Muhammadu Gaskanta ya nemi hadin kan jama’a domin su mara wa ‘yan yankinshi baya wajen samun izinin tsayawa takarar gwamna a shekara ta 2015.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG