YEMEN: 'Yan Tawayen Houthi Sun Yi Hasar Filin Jirgin Sama

Mayaka masu goyon bayan gwamnatin Yemen

Yau Talata sojojin nan masu goyon bayan shugaba Abdu Rabu Mansour Hadi sun sake kame wani sansanin sojan yan tawayen Houthi.

Yayin da suke kokarin ganin sun sauya kanfen din da ya tilasta shugaban barin kasar a cikin watan mayu na wannan shekarar.

Mayakan Masu goyon bayan gwamnati dake da goyon bayan sojojin saman da gwamnatin Saudi kewa jagoranci, sun samu damar kwace filin jirgin saman nan dake kilomita 60 daga tashar jirgin dake birnin Arden.

Wannan wurin mai tasrin nada muhimmaci ga sojojin kasar Amurka musammam akan abinda ya shafi tattara bayanai game da jiragen nan nasu mara sa matuka da suke anfani dasu wajen kai hari a Yemen inda sansanin Al-qaida yake.

Da taimakon sojojin saman da Saudiya kewa jagoranci,da shiga da makamai ta ruwa daga Saudiya, da kuma hadaddiyar Daular Larabawa, wannan na cikn abinda yasa masu goyon bayan gwamnatin suka samu nasarar da suka samu a Aden a cikin watan da ya gabata.

Sai dai har yanzu Hutawan na da ikon wurare masu yawa a cikin Yemen din ciki ko har da babban birnin kasar wato Sanaa wanda suka kwace kusan shekara guda kenan