Shugaban kasa na Iran Hassan Rouhani ya ce yawancin 'yan kasarsa suna goyon bayan yarjejeniyar da kasar ta cimma akan shirin nukiliya da kasashen turai har da Amurka duk da sukar da kafofin labarai su keyi.
A wata fira da yayi da gidan telibijan na CBS a shirin nan mai lakabin 60 Minutes da ake gabatarwa kowane daren Lahadi a Amurka Rouhani yace yawancin hukumomin Iran da suka hada da majalisar wakilai da hukumar tsaro duk sun yi na'am ra'ayin al'ummar kasar akan yarjejeniyar.
Shugaban yace yarjejeniyar nada sarkakiya amma ta dace kuma mataki ne da ya kamata a dauka wajen kawar da kiyayya da rashin amincewa da juna tsakanin Iran da Amurka.
A karkashin yarjejeniyar Iran zata rage inganta yuranium yadda ba zata kaiga kira bam na nukiliya ba. Kasar ta kuma amince da barin sifetoci sa ido akan wuraren da take aikin nukuliyar.
Su kuma kasashen turai da Amurka zasu sassauta takunkumin da suka kakabawa kasar wannda ya raunata tattalin arzikinta.
Wadanda suke adawa da yarjejeniyar musamman kasar Israila suna zargin cewa shirin ya baiwa Iran damar gina bam nan gaba.
Makon jiya 'yan Democrats a majalisar wakilan Amurka suka dakile yunkurin 'yan Republican na yin watsi da yarjejeniyar.