‘Yan jam’iyar Democrat a majalisar dattijan Amurka sun sami kuri’u 41 da suke bukata su takawa masu adawa birki a yunkurinsu na kin amincewa da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da Iran. Wannan na nufin shugaba Barack Obama baya bukatar amfani da ikon gaban kai, abinda ya kasance wata nasara da ya samu a siyasance.
Amurka da wadansu manyan kasashe biyar masu ikon fada a ji, sun cimma yarjejeniyar da Iran a watan Yuli. Yarjejeniyar zata hana Tehran aiwatar da shirinta na nukiliya domin a saka mata ta waje sassauto takunkuma da aka kakaba mata da suka durkusar da tattalin arzikin Iran.
Amurka da abokan kawancenta sun jima suna kyautata zaton cewa, Iran tana amfani da shirin ne wajen kera makaman nukiliya- zargin da Tehran ta musanta.
‘Yan jam’iyar Republican ke da rinjaye a majalisar wakilai a kan jam’iyar Democrat ta shugaba Obama. Ana kyautata zaton majalisar zata kada kuri’ar kin amincewa da yarjejeniyar da aka cimma da Iran, idan basu sami goyon bayan majalisar dattijai ba, kudurin kin amincewar ba zai zama da wani tasiri ba.
Shugaba Obama yayi matukar matsawa ‘yan majalisar lamba su goyi bayan yarjejeniyar, da a yanzu haka suka sami isassun kuri’un da suke bukata su hana ‘yan hamayya takawa yarjejeniyar birki; sai dai yanzu ‘yan majalisa masu hamayya basu da damar tilasawa shugaban kasar amfani da ikonsa na shugaban kasa.