Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai Yi Bayani Akan Shirin Nukiliyar Iran


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Obama zaiyi jawabi a wani lokaci cikin wannan satin domin bayani game da yarjejeniyar da aka cimmawa game da kasar Iran akan batun Nuclear da aka cimma matsaya da ita.

Mai Magana da yawun fadar White House Josh Earnest ya fada jiya Littini cewa Mr Obama zai yi tado da batutuwa masu muhimmamci da yasa yake ganin akwai bukatar goyon bayan wannan yarjejeniyar da aka cimmawa da kasar ta iran.Wanda hakan ya hana ta sarrafa Nuclear a shekaru masu zuwa da musayar dage mata takunkunmin da kasashen yammacin Turai dama MDD suka maka mata.

Earnest yace haka kuma shugaba Obama yana tunanen cewa kamata yayi majilisar dokokin Amurka su marawa kokarin sauran kasashen duniya baya domin ganin an hana kasar Iran sarrafa Nuclear amma ta hanyar difulomasiyya

Mai Magana da yawun fadar White Hiue din yace baya ga wannan tattaunawar da aka yi da kasar ta Iranba wani wanda ya samar da wani tsarin da zai hanakasar ta Iran sarrafa makamin Nuclear ibata hanyar yaki ba.

Sai dai har yanzu majlisar dokokin na Amurka suna cikin kwanaki 60 din su ne na duba wannan yarjejeniyar da aka cimmawa nako su yarda ko kuma a’a, sai dai muddin majilisu dokoki biyu suka sa kafa suka yi fatali da wannan batu shiko shugaba Obama yayi alwashin zaiyi anfani da dinbin ikon da yake dashi domin rattaba mawannan yarjejeniya hannu, wanda hakan zai sa sai sun samu kasha daya cikin ukku kafin su iya rusa wannan dokar.

XS
SM
MD
LG