NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.

Taron nasarori  da aka samu yayin yunkurin magance matsalar yawan matan dake mutuwa sanadiyar zubar da jini a yayin nakuda.

Wata kungiyar kasar Amurka da ake kira Health and Development International ta sanar cewa jamhuriyar Nijer ta samu nasarori  a yunkurin magance matsalar yawan matan da ke mutuwa sanadiyyar zubar da jini a yayin nakuda.

A cewar kwararru wannan shi ne karon farko da ake samun makamancin ci gaban da Nijar din ta samu a fafutikar da hukumar lafiya ta WHO ta sa gaba don takaita mace macen mata a sanadin zubar da jini a lokacin haifuwa dalilin da ya sa kenan kungiyar ta HDI ta ba shugaban kasar Nijar da wasu jami’an kiwon lafiya lambobin yabo.

Taron nasarori da aka samu yain yunkurin magance matsalar yawan matan dake mutuwa sanadiyar zubar da jini a yayin nakuda.

Shugabar kungiyar Health and Developmemt Internatonal wato Tsofuwar jakadaiyar Amurka a Nijer Ambasada Bisa Williams ta yi karin bayani a game da abubuwan da Binciken kungiyar ya gano a asibitoci da dama na sassan Nijar wadanda ke nuna cewa sabon tsarin lafiyar da aka shimfida a wannan kasa daga shekarar 2014 ya taimaka wajen rage yawan matan da ke mutuwa saboda dalilai masu nasaba da zubar da jini a yayin nakuda.

Taron nasarori da aka samu yain yunkurin magance matsalar yawan matan dake mutuwa sanadiyar zubar da jini a yayin nakuda.

Kungiyar ta HDI ta kara da cewa ba a taba samun makamancin wannan ci gaba ba a tarihin fafutikar da aka sa gaba a duniya da nufin murkushe illolin zubar da jini a yayin nakuda kamar yadda aka gani a Nijar.

Wannan ana iya cewa wata hanya ce da kasar Nijar ta bude wa kasashen duniya don magance dadaddiyar matsalar da ke haddasa asarar dimbin rayukan mata a baya.

Ministan kiwon lafiyar al’umma Dr Iliassou Idi Mainassara wanda ke daya daga cikin jami’an lafiyar da aka HDI ta karrama saboda samun wannan nasara na mai alfahari da wannan yunkuri.

Shugaban Kasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda shi ma HDI ta karrama da lambar yabo a yayin bukin gabatar da rahoton binciken kungiyar saboda abinda aka kira dagewarsa akan maganar ceto rayukan mata da yara, ya jaddada aniyar karfafa gwiwa a yaki da mace macen mata da yara kanana.

Saurari rahoton Sule Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Yawan Matan Dake Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu A Nijer