Matan gwamnonin Najeriya sun ce sun dukufa wajen shawo kan yawan matan dake mutuwa lokacin haifuwa.
Alkalumma daga hukumar kiwon lafiya ta duniya sun nuna cewar Najeriya ita ce ta hudu a cikin kasashen duniya wajen samun yawan matan dake mutuwa lokacin da suka zo haihuwa.
Dalilin haka ne uwargidan gwamnan jihar Neja Dr. Amina Abubakar Sani Bello ta kaddamar da wani shiri da aka yiwa lakabin Karama wanda zai maida hankali wajen kula da mata a lokacin da suka zo haihuwa.
Dr Amina ta ce a kokarin shawo kan matsalar a Najeriya duka matan gwamnonin kasar sun bullo da wasu shirye shirye na musamman da zasu kula da mata a lokacin haihuwa.
Uwargidan gwamnan ta yiwa Muryar Amurka karin bayani akan wannan shirin. Ta ce manufarsu ita ce rage yawan matan dake rasuwa idan sun zo haihuwa. Suna fatan mutuwar zata ragu da akalla kashi 75 cikin 100 a wannan shekara.
An baiwa jami'an kiwon lafiya 120 horo na musamman da zasu gudanar da aikin a kananan hukumomi 25 dake jihar kana an raba magunguna na hana zubar jini lokacin nakuda da ma wata riga ta musamman da mace zata sanya domin hana zubar jini kamar yadda Dr Mustapha Jibril Kwamishanan kiwon lafiya na jihar ya yi karin bayani.
Injishi abun da ya sa mata suke mutuwa wajen haihuwa shi ne zuban jini da yawa. Akwai wata kwayar magani idan sun sha kafin su haihu ba zasu zubar da jini fiye da kima ba. Akwai kuma wata roba idan sun sanyata jinin zai tsaya. Haka ma wata riga ta musamman tana tsayar da jinin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum