A ranar Juma’a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki da misalin karfe 7 na safe agogon yankin wato karfe 5 agogon GMT.
An tsara za’a sako rukunin farko na mutanen da aka yi garkuwa da su daga Gaza da misalin karfe 4 na yamma, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Qatar, wacce ke taimakawa wajen tattauna wa a yarjejeniyar.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar Majed Al – Ansari, ya shaida wa manema labarai cewa, yarjejeniyar ta farko tun bayan fara yakin a watan da ya wuce, za ta hada da dakatar da bude wuta a arewaci da kudancin Gaza.
Karkashin wannan yarjejeniyar, za’a sako mata da yara kanana 50 da mayakan Hamas suka yi gaarkuwa da su daga Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, a madadin mata da kanana yara Falasdinawa 150 da aka daure a gidan yari da ke Isra’ila.
A yau Juma’a za’a sako mutum 13 da aka yi garkuwa da su a Gaza, kuma za’a saki Karin wasu rukunin wadanda aka yi garkuwa da su a kowace rana na tsagaita bude wuta har sai an sako jimullar mutum 50.