Yau Shugaba Buhari Ya Gana da Shugaban Amurka Obama

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da shugaban Amurka Barack Obama yau Yuli 20, 2015 yayin da suke ganawa.

A yau shugaban Amurka Barack Obama na karbar bakuncin takwaran aikinsa na Najeriya, Muhammadu Buhari, inda za su tattauna a Fadar White House.

Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya ke ci gaba da zama karfen kafa a Najeriyar, wanda lamari ne da zai mamaye tattaunawar kasashen biyu.

Ana sa ran Shugabannin biyu tare da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, za su tattauna yadda za a samar da sauyi ga siyasa da tattalin arzikin Najeriya, da zimmar dakile matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

Wanna ziyara, wacce zai kwashe kwanaki hudu yana yi, ta kasance ta farko tun bayan da Shugaba Buhari ya lashe zabe a watan Maris.

Fadar White House dai ta jaddada cewa, wannan ziyara wani mataki ne na karfafa dangantakar Amurkan da Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Tasirin Ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari A Amurka - 3'40"