Yau Shugaba Buhari Zai Bude Taron Yaki Da Rashawa a Yola

Karwanê Penaberên Afganistanî li Wanê

A yau talata ne ake sa ran shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai kai ziyarar wuni guda a jihar Adamawa, don bude babban taro kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar ta shirya, inda ake sa ran masana zasu gabatar da kasidu kan hanyoyin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Mataimakin gwamnan jihar Adamawa Mr Martins Babale ya tabbatar da zuwan shugaban kasan a yau Talata, kuma zai zo Yola ne domin aikin wuni guda inda zai bude taro na musamman kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Adamawa ta shirya.

Da yake Karin haske game da damarar da aka yi don tarbar babban makon, Shugaban ma’aikatn jihar Dr. Louis Mandama, yace an yi shirye shiryen da suka kamata don tarbar shugaban kasan. Rundunan yan sandan jihar Adamawa ta bukaci masu ababen hawa da su kauracewa wasu manyan titunan fadar jihar da aka kebe a cewar Othman Abubakar, kakakin rundunan yan sandan jihar.

Da yake taron na yaki da cin hanci da rashawa ne, wasu magoya bayan Shugaba Buhari, kamar irinsu Alh. Suleiman Muhammad Jada, suna ganin akwai bukatar shugaban ya yi tankade da rairaya a cikin wadanda suke tare da shi a yanzu, wanda yace sune su ke bata tafiyar gwamnatinsa.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Zai Yi Tattaki Zuwa Adamawa Yau Talata - 3'13"