Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Sheikh Tureta


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Najeriya ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Abubakar Tureta, wanda Allah ya yi wa rasuwa a Kaduna.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar Sheikh Abubakar Tureta a matsayin wani babban rashi da zai bar gurbi a fagen ilimi.

A wata sanawar da fadar shugaban kasar ta fitar a yau Litinin, kan rasuwar Sheikh Tureta, wacce kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai san zaman lafiya.

“Ya kwashe shekarunsa yana yada sakonnin zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban.” Inji sanarwar.

Buhari ya kuma yi kira ga sauran malaman addini da dalibansa da su rika koyi da abin da ya koyar yana mai fatan Allah ya mai rahama.

“Iya bakin rayuwarsa, ya yi kokari ya kauce wa riginginmu masu raba kawunan jama’a, tare da nuna kyama ga masu yada kalaman batanci.”

Sheikh Abubakar Tureta, wanda fitaccen Malami ne, ya rasu yana da shekaru 74 a Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

A yau Litinin aka yi jana’izarsa a jihar ta Kaduna.

Facebook Forum

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Halin da monoman shinkafa a Zabarmari na jihar Borno ke ciki bayan da mayakan Boko Haram suka kashe kinamin hamsin, da ya sa wasu kaura
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:41 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 3:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG